Kotu ta gargadi Hisbah kan hurumin kama Murja Ibrahim Kunya

murja kunya

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 11 karkashin mai shari’a Nasir Saminu ta yanke hukunci kan karar da Murja Ibrahim Kunya ta kai Hukumar Hisbah da Kwamishian Yan Sandan Kano da Asibitin Dawanau da kuma alkalin kotun shari’ar Musulunci ta Kwana Hudu.

Alfijir labarai ta rawaito cewa Mai shari’a Nasir Saminu ya ce, Hukumar Hisbah ba ta da hurumin kame ko bincike ko gurfanar da wani mutum a Kotu.

Ya ce, aikin Hisbah shi ne wa’azi, amma batun kama mutane da suke yi cushensa aka yi, amma ba bu shi a doka.

Kotun ta kuma yi watsi da gurfanar da Murja da aka yi a Kotun Kwana Hudu inda ta ce hakan ya saba wa doka.

Mai Shari’a ya kuma umarci a gaggauta bai wa Murja Kunya wayarta da katin cirar kudinta na ATM.

Kotun ta kuma umarci Murja Kunya ta biya yan sanda da Asibitin Dawanau Naira Dubu Dari Biyu kowannensu sakamakon ta gaza kawo laifin da suka yi mata a Kotun.

Mai shari’a ya kuma umarci Kwamishinan Yansanda ya kama Murja Kunya idan ta aikata wani laifi na yaɗa abin da ya saɓa wa addini da al’ada.

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *