Alfijr ta rawaito wani gurbatattun magunguna hudu na da nasaba da raunin koda, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Alfijr Labarai
Majalisar Binciken Likitoci ta Gambia ta kuma fitar da sanarwar.
Gambia ta kaddamar da wani binciken gaggawa zuwa gida-gida, bisa zargin wani maganin tari da maganin sanyi da ake kyautata zaton ya haddasa mutuwar yara sama da 60 sakamakon raunin koda a kasar da ke yammacin Afirka.
Daraktan Lafiya Dokta Mustapha Bittaye ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press, cewar, yawan mace-macen yara kanana sakamakon mummunan rauni na koda, lamarin da ya jefa girgizar kasa a fadin kasar mai mutane miliyan 2.4 da ma duniya baki daya.
Alfijr Labarai
“WHO ta fitar da sanarwar gargadin magunguna guda hudu da aka gano a Gambiya wadanda ke da alaka da munanan raunukan koda da kuma mutuwar yara 66, kamar yadda Darakta-Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a cikin wata sanarwa da aka bayar Laraba. ”
Magungunan guda hudu sune tari da maganin sanyi da ake samarwa a Indiya, in ji sanarwar ta WHO.
Yayin da ya zuwa yanzu an gano gurbatattun kayayyakin a Gambiya, mai yiwuwa an rarraba su zuwa wasu kasashe, in ji shi.
Hukumar ta WHO tana bin diddigin bincike tare da kamfanin da hukumomin da ke da tsari a Indiya, in ji ta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller