Mutum Biyu Sun Rasu, An Ceto Bakwai A Hadarin Jirgin Ruwa A Jigawa

Alfijr ta rawaito mutane biyu 2, sun rigamu gidan gaskiya, bayan da aka ceto mutane bakwai 7 a wani hadarin jirgin ruwa da ya afku a garin Miga ta jihar Jigawa

Kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam ne ya bayyana afkuwar hadarin a lokacin da manoma tara ke dawowa daga gonakinsu a Galauchime zuwa kauyen Sansani a karamar hukumar Miga.

Shisu ya ce da isar manoman kogin, sai suka hau wani kwale-kwalen da wani mai suna Ado Dan Maguga yake tukawa amma abin takaici sai kwale-kwalen ya kife saboda ruwan sama da iska da ake ta fama.

“An ceto mutane bakwai yayin da sauran biyun suka bata.

Alfijr Labarai

“Mutane biyun da aka samu gawarwakin su Imran Rabiu, dan shekara 12; da Tasiu Rabiu mai shekaru 14. An gano gawarwakinsu daga baya aka mika wa iyalansu domin yi musu jana’iza.”

Slide Up
x