Alfijr ta rawaito Wani matashi dan shekara 25 mai suna Ammar Ibrahim ya nutse a wani kogi a kauyen Tattarawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Alfijr Labarai
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Abdullahi ya fitar a yau Laraba a Kano.
Lamarin ya faru ne a jiya Talata, in ji sanarwar
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:34 na safe daga wani Muhammad Sani kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:55 na safe.
“Direban Adaidaita sahu din da ke kan hanyarsa ta komawa Kano, ya yi fakin a gefen titi kusa da wani kogi da nufin wanke babur din, amma sai tsautsayi ya ja shi cikin kogin.
“Ya yi ƙoƙari da yawa don ya tsira amma hakan bai yiwu ba,” in ji Abdullahi.
Alfijr Labarai
An fito da marigayi Ibrahim daga cikin ruwan a sume kuma daga baya aka tabbatar da rasuwar sa bayan kokarin cotonsa
Abdullahi ya ce an mika gawar ga Sifeto Jerry Mathew na ofishin ‘yan sanda na Dawakin Tofa.