Na shirya tsaf don fasa ƙwai kwananan – In Ji Baffa Bichi Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano

FB IMG 1736504630562

Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, SSG, Dakta Baffa Bichi ya ce yana da ajuyayyun ƙwararan hujjoji a kan gwamna Abba Kabir Yusuf da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da zai fito da su nan gaba kaɗan.

Wannan shi ne karo na farko da Bichi ya yi magana tun bayan cire da gwamnan Kano ya yi a matsayin sakataren gwamnati.

Da ya ke magana ga magoya bayan sa a juya Alhamis bayan ya dawo daga Umrah, Bichi ya ci alwashin tona asiri, inda ya ce ya na da hujjoji da shaidu na badaƙala da a ka yi a gwamnati.

“Na gode Allah na gama lafiya. Wannan ba lokacin magana ba ne amma ina da hujjoji ƙwarara da zan fasa ƙwai. Zan tona asiri don mutane su san ko su wadanne irin mutane ne.

“Maciya amana ne kuma butulaye ne. Mun taimaka musu amma sun mana butulci amma ba komai, za mu tona musu asiri,” in ji Bichi, da ake ganin da Abba da Kwankwaso ya ke.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *