“Najeriya Akwai Kudi” Tuggar Ya Maida Martani Kan Tafiye-tafiyen Tinubu Zuwa Kasashen Waje.

IMG 20250127 WA0195

Daga Aminu Bala Madobi

Ministan harkokin kasashen ketare ya ce Bulaguron shugaban kasar abune da ya zama wajibi, domin yana bukatar mu’amala da shugabannin wasu kasashe.

Rahotonni sunce wasu ‘yan Najeriya dai sun fusata kan yadda Shugaban kasar ke yawaita yin balaguro daga kasa zuwa kasa, yana barnatar da kudaden masu tarin yawa duk da sunan neman masu zuba jari zuwa Najeriya.

Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, rahotanni sun ce Tinubu ya ziyarci kasashe kusan 19 a tafiye-tafiye 32 na kasashen waje.

Tun daga watan Agustan 2024, Tinubu ya kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 2.3 wajen tafiye-tafiyen kasashen waje da kuma abubuwa masu alaka da hakan cikin watanni shida kacal.

An bayyana wannan kididdiga ne cikin bayanan da aka samu daga GovSpend, dandalin nazari na gudauniyar BudgIT Foundation, me binciken kwakwaf.

Bayanai sun nuna cewa a tsakanin 21 ga watan Fabrairu zuwa 19 ga watan Yulin 2024, shugaba Tinubu ya lashe makudan kudade har Naira miliyan 2,346,623,000 a matsayin kudaden balaguron da ya ke kashewa tun bayan hawansa mulki.

A cewar GovSpend, a ranar 21 ga Fabrairu, 2024, fadar gwamnatin tarayya, ta biya Naira miliyan 300 na tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da suka danganci hakan na watan Janairu 2024.

A ranar 24 ga Fabrairu, 2034, hedkwatar gidan gwamnati ta kuma biya N250,000,000 na tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da suka jibanci haka. Kuma a ranar 15 ga Maris, 2024, an biya Naira miliyan 42,379,100 don tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da suka danganci hakan.

Sannan A ranar 15 ga Maris, 2034, an biya Naira 9,484,310 na tafiye-tafiyen shugaban kasa. Sannan kuma an biya Naira miliyan 25,393,490 na tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da suka jibanci, sannan an biya wani Naira miliyan 34,185,400 a daidai wannan ranar.

An kuma biya Naira 5,602,600 daga gidan gwamnati zuwa wasu asusu gidan gwamnati – inda aka biya wasu kudade – don tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da tafiye tafiyen suka kunsa.

A ranar 15 ga watan Maris, an sake biyan Naira miliyan 106,422,600 na tafiye-tafiyen shugaban kasa, sannan kuma an biya wani Naira miliyan 5,505,100 a daidai wannan ranar.

Haka kuma an biya Naira 5,001,700 na tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da suka jibanci hakan a ranar 15 ga watan Maris.

Haka kuma an biya N65,474,000 a ranar 15 ga watan Maris, daga hedikwatar gidan gwamnatin jihar zuwa hedikwatar fadar gwamnati da aka biya don tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran abubuwan da suka shafi hakan. An kuma biya wani N300,000,000 mai taken, “Biyan tafiye-tafiyen Shugaban kasa a watan Maris”.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇

https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *