Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa Najeriya na rasa sama da Naira biliyan 40 duk shekara saboda damfara da ake yi ta daukar ma’aikata.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata ganawa da jami’an Kungiyar Tattaunawa da Ma’aikata ta Najeriya (NECA) a hedkwatar EFCC da ke Abuja.
Shugaban EFCC ya ce binciken da ya gudanar a shekarar 2007 kafin ya shiga hukumar, ya gano cewa ma’aikata suna cutar juna ta hanyoyi daban-daban.
“A shekarar 2007, kafin na zo EFCC, na yi bincike kan damfara a daukar ma’aikata, inda na bincika yadda masu daukar aiki ke damfarar ma’aikata, da kuma yadda ma’aikata ke damfarar kamfanoni da hukumomi da suke aiki a cikinsu. Tun a wancan lokacin na gano cewa Najeriya na asarar sama da Naira biliyan 40 duk shekara saboda wannan matsala,” in ji Olukoyede.
Ya ce tun bayan hawansa shugabancin EFCC, hukumar ta ceci miliyoyin nairori bayan ta gano cewa akwai dimbin marasa aiki da ke karbar albashi daga gwamnatin tarayya.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ