Najeriya Ta Hana Amfani Da Dala A Ofisoshin Jakadun Ƙasashen wajenta

Screenshot 2024 02 27 13 29 28 70 b86672daa061159f52c1a3195c773d05 edit 485116325967

Najeriya ta hana ofisoshin jakadun ƙasashen waje amfani da kuɗaɗen ƙasashen waje don gudanar da ayyukan neman takardun biza da sauran harkokinsu

Ƙasar- da ke fama da matsalar karyewar kuɗinta wato naira b- ta umarci ofisoshin jakadun ƙasashen wajen su riƙa amfani da kuɗin ƙasar wajen gudanar da hada-hadarsu.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar Yaƙi da ya yi wa Tattalin Arzikin Najeritya Ta’annati ta EFCC, ta ce an ɗauki matakin ne domin magance mamayar da dala ta yi wa harkokin tattalin arzikin ƙasar, tare da karyewar darajar kuɗin ƙasar, wato naira.

EFCC ta bayyana hada-hada da kuɗin ƙasashen waje da ake yi a ofisoshin jakadun wajen a matsayin wata barazana ga tattalin arzikin ƙasar, da ƙarfi ko kimar ƙasar.

Abaya-bayan nan Najeriya ta fuskanci hauhawar farashin kayyaki tare da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da ba a taɓa gani ba, musamman a shekarar da muke ciki.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *