“Nasan Me Sauyawa Ribadu Daloli Na Cin Hanci Da Rashawa” – Amma fa in ji Dr Idris

IMG 20250206 WA0251

Daga Aminu Bala Madobi

Fitaccen mai bincike kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a ɗan asalin Najeriya, mazaunin kasar Ingila, Dr. Idris Ahmed ya bayyana wasu muhimman zarge-zarge da ya sani akan Malam Nuhu Ribadu mai taimakawa Shugaban kasa kan sha’anin tsaron Najeriya.

Alfijir labarai ta rawaito Dr. Idris ya bayyana cewa, “A lokacin da yake Shugabancin hukumar EFCC, ya karbi makudan kudaden cin hanci. Musamman dalar Amurka, akwai wani wanda Shi ne me yiwa Nuhu Ribadu canjin dalar Amurka, wanda tsohon dan sanda, ne ACP mai ritaya ne ana kiransa da suna (retired) Rabiu Abubakar Shariff.

Rabiu Abubakar Shariff shi clasmate dina ne lokacin muna karatun sakandare. Shine wanda Lieutenant General Tukur Buratai ya turo shi zuwa kasar Burtaniya, domin ya saci salulata. Wanda Bai yi nasaran yin hakan ba Har Allah ya tona masa asiri. amma sunyi nasaran hacking salulan daga bisani.

Binciken ya nuna cewa alokacin da Rabiu yake canjawa Ribadu kudi a kasuwan canjin dollar dake Obalande Lagos, yana zaune ne a boys quarter na gidan babban yayanmu, marigayi injiniya, Ahmed, a Victoria Island, dake Legas,

Wannan shi yasa nake da cikakken bayani game da jagwal da Malam Nuhu Ribadu yayi da Rabiu Abubakar Shariff mai canjin dala.

Yanzu haka da muke magana, Rabiu Abubakar Shariff shine mai baiwa Nuhu Ribadu shawara akan tsaro!

Jama’a, da irin wannan shugaban kasan, da NSO nashi, da mai baiwa NSO shawara akan tsaro, ta ina ne Najeriya zata ci gaba? Dukkansu ukun azzalumai ne, maciya amanan Najeriya da al’ummanta.  Inji Dr. Idris Ahmad.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *