Tinubu ya sallami A’isha Maikudi a matsayin shugabar jami’ar Abuja

FB IMG 1738869736028

Daga Aisha Salisu Ishaq

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami’o’in gwamnatin tarayya da dama da su ka hada da Jami’ar Abuja l, wacce a yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon. Waɗannan canje-canjen sun fara aiki na nan take.

A Jami’ar Yakubu Gowon, wacce a da sunan ta Jami’ar Abuja, Tinubu ya rusa majalisar gudanarwar jami’ar baki daya tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga mukaminta na shugabar jami’ar inda aka maye gurbin ta da Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin riko na tsawon watanni shida.

Sanata Lanre Tejuoso, wanda a halin yanzu shine babban shugaba a Jami’ar Aikin Gona ta Makurdi,  an kai shi Jami’ar Yakubu Gowon s matsayin Babban Shugaba jami’ar.

Sanata Joy Emordi, wacce a yanzu ita ce shugabar jami’ar ilimi ta Alvan Ikoku za ta gaje shi a Makurdi.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *