NBC Ta Ci Tarar Arise TV Zunzurutun Naira Miliyan 2

Alfijr ta rawaito hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta Najeriya NBC, ta ci tarar gidan Talabijin na Arise TV, Naira miliyan biyu bisa zargin yaɗa rahoton ƙarya wanda saɓa ƙa’idojin yaɗa labarai.

Hukumar ta rubuta wa gidan Talabijin ɗin takarda ne inda a ciki umarce ta da ta biya kuɗin tarar.

A ƙarshen makon da muka yi bankwana da shi ne aka yi ta yaɗa Labarin cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC tana binciken shari’ar da ta shafi Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a kasar Amurka.

Sai dai hukumar zabe ta musanta wannan ikirarin, in da ta bayyana wata takarda da ke yawo wanda ke dauke da hujjoji tare da wasu bayanan da ake zargin Tinubu da dillacin kwayoyi a amurka a matsayin “karya”.

Da take maida martani, kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC ya bukaci NBC da ta sanya wa kafafen yada labaran da suka yada rahoton takunkumi.

Sai dai a jiya Litinin babban daraktan hukumar ta NBC Malam Shehu Illelah ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

“A ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba, hukumar ta bibiyi yadda aka yi amfani da sanarwar manema labarai da aka ce Mista Festus Okoye, kwamishinan labarai na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ya fitar, inda tashar Arise TV ta yada.

“Sanarwar da aka rabawa manema labarai ta yi zargin cewa hukumar zabe na gudanar da bincike kan batun sharia da wata kotun Amurka ta yi kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, da nufin gurfanar da shi a gaban kotu.

“Hukumar zaben ta yi watsi da sanarwar, inda tace babu kamshin gaskiya kan yadda ake alakanta sanarwar ga hukumar, karya ce zalla”

Idan za a iya tunawa, Illelah a tsakanin ranakun 19 zuwa 26 ga Satumba, 2022, ya karade kasar nan domin wayar da kan masu yada labarai tare da tunatar da su tanadin kundin tsarin yada labarai na Najeriya da kuma dokar zabe yayin da kasar ke dab da babban zabe na 2023.

Illelah ya ce hukumar tare da masu ruwa da tsaki sun dukufa wajen ganin an gudanar da zabukan 2023 cikin gaskiya da adalci, ya kuma bukaci kafafen labarai da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin kwarewa, domin a samu nasarar gudanar da tsarin dimokuradiyya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *