NDLEA Ta Kama Mutane 6 a jami’ar Bayero kan zargin safarar muggan kwayoyi

IMG 20241124 123555

Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen rundunar Kano ta gudanar da wani samame a tsohuwar Jami’ar Bayero Kano (BUK Old Site), inda ta kama mutane 6, da ake zargi da hannu a harkokin miyagun kwayoyi tare da rusa wasu maboyarsu.

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan wata korafi a hukumance da mahukuntan jami’ar Bayero Kano suka gabatar mata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadi Muhammad maigatari ya sanyawa hannu a yau Litinin.

A karkashin shirin “Operation Sharar Mafaka”, jami’an NDLEA sun kai samame domin fatattakar mutanen da suka mayar da wasu sassan harabar jami’ar wajen safarar da kuma shan miyagun kwayoyi.

A yayin samamen, an kama mutane shida da ake zargi, tare da kwace wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da wadannan haramtattun ayyuka, inda aka lalata su domin hana ci gaba da amfani da su.

Da yake jawabi kan nasarar aikin, shugaban rundunar ta NDLEA a Kano , CN DY Lawal, ya ce wannan mataki na nuna kudirin hukumar wajen tabbatar da samar da muhalli mai tsabta daga miyagun kwayoyi domin dalibai, ma’aikata da iyalansu su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Za mu ci gaba da fatattakar dukkan maboyar miyagun kwayoyi a karkashin Operation Sharar Mafaka,” in ji shi.

Har ila yau, wannan samame ya nuna muhimmancin hadin gwiwa tsakanin NDLEA da hukumomin ilimi, inda kai rahoton da wuri da hadin kan jami’ar ya taimaka wajen daukar mataki cikin gaggawa domin kawar da barazanar da ke addabar tsaron harabar makaranta da al’umma baki daya.

Hukumar NDLEA ta Kano ta sake gargadin duk wanda ke amfani da cibiyoyin gwamnati ko na ilimi wajen safarar ko shan miyagun kwayoyi da cewa ba za a lamunci irin wadannan ayyuka ba. Har ila yau, ta bukaci al’umma da cibiyoyi da su rika kai rahoton duk wani abu da ake zargi domin gano sauran maboyar masu laifi da kuma kawar da su baki daya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *