Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce nan gaba kaɗan zai bayyana matsayinsa kan shirinsa na sauya sheƙa daga Jam’iyyar ADC
Sanata Kwankwaso ya sanar da haka ne a daren Asabar, a yayin da yake ƙarin haske kan lamarin, bayan rahotanni sun bayyana cewa zai koma Jami’yyar NDC bayan ficewa daga ADC.
Ya bayyana cewa, har yanzu ba a riga a yanke wani hukunci na ƙarshe ba kan makomar siyasarsa da ta abokan tafiyarsa, amma nan gaba za su sanar da matsayin da suka ɗauka.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa suna ci gaba da tattaunawa da wasu jam’iyyu, ciki har da NDC da PRP da sauransu domin yanke hukunci mafi amfani ga makomar siyasarsu.
Da yake ƙarin haske kan dalilin tunaninsu na ficewa daga ADC, Kwankwaso ya ce, duk da cewa hukuncin Kotun Ƙoli na baya-bayan nan ya tabbatar da sahihancin Kwamitin Rikon Ƙwarya na Jam’iyyar ADC, ƙarƙashin jagorancin David David Mark, amma kuma kotun ta a mayar da batun zuwa Babbar Kotun Tarayya.
Wannan, a cewarsa, ya jefa jam’iyyar ADC cikin tsaka mai wuya, saboda Babbar Kotun Tarayyar ta riga ta yanke hukunci da ya soke taron gangamin jam’iyyar na baya-bayan nan.
Ya ce, bugu da ƙari, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya shigar da ƙara a kotu yana a soke rajistar Jam’iyyar ADC baki ɗaya.
Kwankwaso, ya tuna da cewa sun bar Jam’iyyar NNPP ne saboda matsalolin shari’a da suka dabaibaye ta —wanda ya sanya zama a cikin jam’iyyar ya zama kasada.
Jagoran Kwankwasiyyan ya bayyana cewa ce, yanzu kuma ADC ta tsinci kanta cikin irin wannan hali, wanda ya sa suka fara tuntuba da shugabannin NDC, PRP da sauran jam’iyyu —kamar yadda sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar ke yi—domin duba hanyoyin da suka fi dacewa wajen kare muradun dimokuraɗiyya.
Ya ce za su sanar da matsayinsu a nan gaba kadan.
Batun takarar Kwankwaso
Kan batun nema takarar shugaban ƙasa, Kwankwaso ya tuna tarihinsa a siyasa inda ya ce a zaben fid-da-gwani gwani na jam’iyyar APC a 2014 ya zo na biyu bayan Muhammadu Buhari, inda Atiku Abubakar ya zo na uku, Rochas Okorocha ya zo na huɗu, sannan marigayi Sam Nda-Isaiah na biyar.
Haka kuma a 2019 ya nemi tikitin PDP amma bayan ya rasa, ya mara wa Atiku Abubakar baya, wanda ya lashe, inda Kwankwason ya zama mai kula da yaƙin neman zaɓen Atiku a Arewa.
A cewar Kwankwaso, wannan ya isa shaida a kan cewa a koyaushe yana fifita muradun ƙasa da haɗin kan jam’iyya fiye da son zuciya.
Ya bayyana cewa har yanzu ADC ba ta keɓe yankin da zai ba wa tikitin takarar shugaban ƙasa ba, ko ɗan takara. Don haka bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, kuma bai mara wa wani mai neman takarar baya ba, duk wata jita-jita akasin haka ba ta da tushe.
Ya kuma bayyana cewa rashin halartarsa tarurrukan jiga-jigan ADC na baya-bayan nan ya samo asali ne daga dalilai na sirri da ba zai iya kauce wa ba, inda ya aika da uzurinsa ga shugabancin jam’iyyar.
A karshe, Kwankwaso ya tabbatar da cewa za su ci gaba da shiga tattaunawa a dukkan matakai, kuma duk wani matsayi na ƙarshe kan makomar siyasarsu, za a sanar da shi ta hanyar hukuma a lokacin da ya dace.
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t