NLC Ta Maidawa DSS Martani Akan Maganar Zanga-zanga

FB IMG 1708598672316

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa, NLC, ta caccaki hukumar tsaro ta farin kaya, SSS kan kiran ta ga kungiyar da ta janye zanga-zangar da take shirin yi.

Alfijir labarai ta rawaito Kungiyar ta NLC ta dage cewa za a gudanar da zanga-zangar adawa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.

Rahotanni sun bayyana cewa, gazawar gwamnatin tarayya na cika alkawuran da ta dauka bayan wa’adin kwanaki 14 na kungiyar kwadago ne ya sanya za ta fuskanci yajin aikin.

A jiya Laraba ne mai magana da yawun hukumar SSS, Peter Afunanya, ya bukaci kungiyar ta janye shirinta na zanga-zanga domin zaman lafiya a kasa.

Ma’aikatar ta bukaci kungiyar da ta ci gaba da tattaunawa da sasantawa maimakon shiga halin da ka iya tada hankali.

Sai dai shugaban NLC, Joe Ajaero, a wata sanarwa da da kansa ya sanya wa hannu a yammacin Laraba, ya ce babu gudu babu ja da baya a yajin aikin.

Ajaero ya yi tambaya kan dalilin da ya sa har yanzu hukumar SSS ba ta kama masu shirin kawo wa zanga-zangar naƙasu ba.

“Ba za mu iya naɗe hannayenmu mu yi kamar cewa komai ba tafiya dai-dai ba. Hakan zai zama mummunan makirci da tarihi ba zai yafe ba,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *