Captain din Super Eagle Ahmad Musa ya kai ziyara ta musamman a fadar mai martaba sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero.
Ahmad Musa ya bayyanawa Mai Martaba sarkin Kano cewar ya shirya bawa asibitocin Jihar 44 tallafin kayayyakin duba marasa lafiya don kulawa da marasa lafiya nan da zuwa kafin Azumin watan Ramadan.
A nasa jawabin mai Martaba ya yi farin ciki da Sanya albarka Kan wannan yunkuri. Sannan yayi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da Ahmad Musa wajen aikin alheri.
Sannan Mai Martaba sarkin Kano ya shawarci matasa da su dauki harkar kwallon kafa a matsayin sana a, suyi koyi da Ahmad Musa.
A karshe Musa yace “Ina cike da farin ciki sosai yadda aka tarbe mu a masarautar.”
Zanyi amfani da wannan dama domin in mika sakon godiya ga Sarkin kano da dukkanin masarautar da jama’ar Jihar kano baki daya.
Nagode ❤️🙏




Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V