
Alfijr ta rawaito jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano ta musanta labarin da ake yaɗa wa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya hana Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf rushe gine-ginen da yake yi.
A zantawarsa da Freedom Radio lauyan jam’iyyar Barrister Bashir Muhammad Tudunwuzirci ya ce labari ne na ƙanzon kurege.
Ya ƙara da cewa Shuagaban ƙasa ba shi da hurumin hana Gwamna aiwatar da tsare-tsaren yadda yake son yi da ƙasa a jiharsa.
Ya kuma zargin ƴan Jami’yyar APC masu adawa da yaɗa wannan labarin na ƙarya.
Barrister Tudunwuzirci ya ce, rushe-rushen da Gwamnatin NNPP ke yi tana yi ne don sake gyara Kano ba wai don ɓarna ba, kuma ba gudu ba ja da baya a kai.
Freedom Radio
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ