
Alfijr ta rawaito Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya sa baki kan rusa gine-ginen da ake yi a Kano bayan wata ganawa da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin daren ranar Asabar ya rusa wasu gine-gine a Otal din Daula da kuma sansanin Hajji da ke cikin birnin Kano.
Gine-gine na miliyoyin nairori sun lalace kamar dai yadda gine-gine masu hawa uku na farko da shaguna 90 a kan titin Race Course, a unguwar GRA ta Nasarawa, wanda ke nuna gine-ginen da gwamnati ta kira haramtacce.
A ranar Asabar ne Gwamna Yusuf ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da rusa gine-ginen da gwamnatin ta yi imanin cewa haramun ne a jihar.
Idan dai ba a manta ba tsohuwar gwamnatin Ganduje ta ce ginin da aka gina a Otal din Daula shiri hadin gwiwa ne da jama’a.
Wani kamfani mai suna Lamash Properties Limited, ya sha alwashin kalubalantar rushe otal din Daula da gwamnatin jihar Kano ta yi inda ya bukaci a biya Diyyar N10bn a aikin.
LAMASH Properties Limited, wani kamfani ne na raya kadarori da gwamnatin jihar Kano ta gayyace shi tare da wasu kamfanoni a wasu lokutan a karshen shekarar 2020 domin neman sake gina tsohon otal din Daula da ke karkashin wata kamfani mai zaman kansa.
Wannan ya biyo bayan tsohon gwamna Ganduje ya garzaya don ganawa da shugaba Tinubu domin yi masa bayani kan lamarin.
A cewar majiyoyin fadar Villa, shugaban ya damu matuka da asarar biliyoyin Naira da wasu mutane suka yi saboda rugujewar ginin.
“Tinubu ya ba da umarnin a dakatar da rushewar saboda rashin hankali ne kuma yana haifar da asara ga ‘yan Najeriya,” in ji majiyar da ta so a sakaya sunanta.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su dakile duk wani barna a Kano.
Majiyar ta kara da cewa, “Wannan ne ya sa gwamnan ya tsaya da rugujewar da ake yi saboda rahoton tsaro da jami’an tsaro suka gabatar masa.
Da aka tuntubi ko gwamnati za ta ci gaba da rusa ginin, Tofa ya shaida wa jaridar cewa: “har yanzu ana ci gaba da rusau, gwamnati ta kuduri aniyar kwato kadarorin jama’a da aka sayar ko aka ware.”
Ya kara da cewa, “Wannan aikin yana da matukar amfani ga jama’a, za a kai ga cimma matsaya mai ma’ana in sha Allahu,” in ji shi.
Politics digest
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ