
Alfijr ta rawaito Hukumar tsaron fararen hula ta Ƙasa, NSCDC, reshen jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da ƙwacen waya.
Ibrahim Idris Abdullahi, mai magana da yawun rundunar, a yau Laraba ya bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka: Faisal Usman, mai shekaru 28, Mansur Isa, mai shekaru 38, Abdullahi Bashir, mai shekaru 25, Ahmed Ibrahim, 21 da Zulkifil Bello, mai shekaru 25, inda ya ce dukkan su sun kware wajen ƙwace da satar wayoyi.

“Wadanda ake zargin na yin laifukan ne a yankin unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge a jihar, inda suke sata tare da kwace wayoyin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
“Jami’an mu na sashen leken asiri da binciken sirri na kan hanyar kamo wadanda ake zargi abokan laifin wadannan ne da su ka hada da wani mutum mai suna Mista Sunday da Abdullahi, wadanda suke sayar da wayoyin da kuma katin SIM,” in ji shi.

Kakakin ya ce an kwato kayayyakin da suka hada da wayoyin hannu guda uku da tarin makullai daga hannun wadanda ake zargin.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ya kara da cewa, “da zarar an kammala, za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.”
Mista Idris-Abdullahi ya ce rundunar za ta ci gaba da yaki da satar waya da aikata laifuka, da kuma kare muhimman kadarorin kasa da kayayyakin more rayuwa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇