Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya shigar da karar Anthony Aziegbemi, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Edo a gaban kotu.
Alfijir Labarai ta rawaito matakin shari’ar ya biyo bayan zargin da Aziegbemi ya yi, inda ya ce fadar shugaban kasa ta hannun hukumar NSA da kuma hukumar DSS na shirin yin magudi a zaben gwamna da ke tafe a jihar Edo.
A cikin wata sanarwa mai taken *Edo 2024: Yunkurin Fadar Shugaban Kasa Kan Katsalandan, Manipulate Zaben Guber Ta Amfani Da DSS, NSA Uncovered,* Aziegbemi ya zargi Ribadu da bayar da izinin sakin dala miliyan biyu ga dan takarar jam’iyyar APC domin sayen kuri’u da kuma bayar da cin hanci ga hukumomin tsaro.
A martanin da suka mayar, Wakilan Lauyoyin Ribadu, Charles Musa & Co., sun fitar da wata takarda inda suka yi Allah-wadai da ikirarin, inda suka bayyana cewa zargin ya yi wa Ribadu mummunar illa. Marian Aigbedion wacce ta sanya wa hannu a madadin kamfanin, wasikar ta bayyana cewa zargin ba shi da tushe balle makama kuma kai tsaye ya ci karo da alkawarin da Ribadu ya dade na tabbatar da gaskiya da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj