Daga Aminu Bala Madobi
Kungiyar Kano Online Media Chapel (KOMC) ta bai wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Lambar Girmamawa, bisa gagarumar gudunmawar da gwamnatinsa ke bayarwa wajen sake inganta kwarewa, nagarta da da’a a aikin jarida, musamman a bangaren jaridar yanar gizo a fadin jihar Kano.
Jaridar Alfijir labarai ta rawaito karramawar ta zo ne sakamakon tsare-tsare da manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samar na daukar nauyin bada horon kwanaki biyu ga ‘yan jaridar yanar gizo da ya gudana a Dutse, tare da ba su cikakken goyon baya wajen gudanar da aikinsu cikin kwarewa da rikon gaskiya.
Da yake bayyana dalilan karramawar, Shugaban kungiyar, Kamaret Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da martabar aikin jarida ta zamani, inda ya bai wa ‘yan jaridar yanar gizo muhimmanci a tsarin sadarwa da wayar da kan al’umma kan manufofi da ayyukan gwamnati.
Ya ƙara da cewar Gwamna Yusuf na da fahimta mai zurfi kan rawar da kafafen yada labarai na yanar gizo ke takawa a wannan zamani na fasaha, ta hanyar bude kofar hadin gwiwa, tallafa wa shirye-shiryen horaswa, da kuma karfafa bin ka’idojin aiki da gujewa yada labaran karya.
Dangambo ya kara da cewa goyon bayan gwamnan ya ba wa ‘yan jaridar yanar gizo kwarin gwiwa, tare da sake hura musu numfashin kwarewa, kirkira da kishin gaskiya wajen gudanar da ayyukansu, lamarin da ya taimaka wajen inganta sahihin bayani da zaman lafiya a jihar Kano.
A cewarsa, karramawar na kuma nuna yadda Gwamnan ke mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin aikin jarida, tare da daukar kafafen yada labarai a matsayin abokan hulda na gaskiya wajen gina al’umma mai wayewa.
Da yake maida jawabi, Kamaret Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan yada labarai da harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, wanda ya karɓi lambar yabon a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano ta tanadi tsare-tsare masu yawa da za su ƙara inganta haɗin gwiwa da ‘yan jarida, inda ya jaddada cewa ‘yan jarida abokan tafiya ne wajen wayar da kan al’umma da ci gaban jihar.
“Yan jarida abokan tafiya ne, wajan tabbatar da cigaba da ya shafi mulki dake taimakawa wajan tabbatar da Gwamnati nayin abinda ya kamata” Acewar Waiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t