Jami’an tsaro sun Kama Wani mutum mai sana’ar siyar da kayan miya, bisa zarginsa da binne mutane a gidan sa dake garin Yarbarau, a Karamar hukumar Dawaki Kudu ta jahar Kano
Alfijir labarai ta ruwaito ana zargin mutumin ne da laifin yin garkuwa da mutane, idan ba a kawo kudin fansa ba, sai ya kashe su, ya binne a cikin gidan kamar yadda wasu daga cikin mazauna yankin Suka bayyana.
Wasu ganau sun Kara da cewa, an samu gawar mutane uku a gidan, kuma tuni Suka yi gangami tare da rushe gidan baki dayansa.
Wani matashi ya ce suna zarginsa da laifin sace yan uwansa da wasu mutane, bayan da Jami’an tsaro suka zo gudanar da bincike ne aka gano Wani rami dauke da mutane a cikin buhu.
Wani Mazaunin garin, ya ce ji aka yi wari yana tashi a gidan shi yasa ma aka balle kofar gidan har ma’aikata suka zo suka gudanar da binciken gano gawarwakin mutanen.
Al’ummar yankin sun yi tired da alawadai tare da kira da a hukunta dukkan wadanda suke da hannu wajen aikata wannan rashin imani.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj