“Rasuwar Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Duniyar Musulunci” – Shugaban Asibitin Best Choice

IMG 211353 271125 1764274452729

Hukumar Gudanarwar Asibitin Ƙwararru Na Best Choice Dake Kano ta bayyana rasuwar fitaccen malamin addini, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a matsayin babban rashi da ya girgiza duniyar Musulunci baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Asibitin Alh Auwal Muhammad Lawal (Dan Malikin Garo) ya aikewa Alfijir, Kwaramet Lawan yace Sheikh Dahiru ya kasance haske ne ga al’umma, kuma jagora abin koyi, kuma ginshikin da Musulmai ke alfahari da shi wajen ilimi, tarbiyya da zaman lafiya.

Kwamaret Lawan ya ce babu shakku lokacin da labarin rasuwar Babban Malamin ta iske su, sun shiga rudani da jimami matuka la’akari da kusan kowa yasan irin gudunmawar da malamin ke bayarea ga duniyar addini da ƙasa baki daya.

Shugaban asibitin daganan ya jaddada cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya shafe rayuwarsa ne wajan hidimtawa addini da gina mutane ta hanyar Alƙur’ani da koyarwar Manzon Allah, wanda hakan ya sa mutuwarsa ta bar babban gibi wanda zaiyi wuya a iya cike shi cikin sauƙi.

Shugaban Asibitin na Best Choice daga nan ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin da rahama, ya ba iyalansa da mabiyansa haƙurin jure wannan babban rashi, tare da roƙon Allah ya cigaba da raya koyarwar da Shehin Malamin ya bari domin al’ummar Musulmi su ci gaba da amfana da ita.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *