A wani binciken ƙwaƙwaf da jaridar Alfijir labarai ta gudanar a fadin kasuwannin jihar Kano, da wasu makwaftanta, mun gano irin yadda kamfanunuwan fulawa da manyan dilolinta suka ji kiraye-kirayen al’umma wajen sauko da farashin fulawar, wanda kowa ya sani sai da farashinta ya kai ₦82,000 ta dawo ₦80,000 ta sake dawowa ₦74,000 a baya, amma yanzu haka ana siyar da ita Naira 62,000, wasu ma suna rage wani abin a kan haka! Allah ya saka muku da alheransa ameen.
Sai dai kuma Rijiya ta bada ruwa guga ya hana, a wani samfurin zaurance irin na ɗan Hausa.
Abin takaici a nan shine, lokacin da masu ruwa da tsaki akan fulawa suka kara kuɗi nan da nan masu sana ar sarrafa Fulawar suka dinga guna guni akan ƙarin, wasu ma har da zanga-zanga akan anyi musu kari, do kai a rage ko kuma shu shiga yajin aiki ko kuma su kara kuɗi.
A karshe dai sun ƙara kuɗi yadda suke so duba da farashin da suka ce an karawa fulawar.
To yanzu dai ta faru ta kare, karshen tuka tuki tik! Farashi yayi kasa yadda ya kamata, menene dalilinku na kin sauke farashin tunda a baya kunce karin?
Masu burodi, masu Gurasa, masu Waina, masu Fanke, masu Cincin da sauran masu sana a da fulawa kuji tsoron Allah ku tuna fa yana karɓar addu’ar wanda aka zalinta tun a duniya fa.
A karshe muke nasihar muyi koyi da fadin Annabinmu Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallama na cewar ku zama daga cikin masu saukakawa al’umma wajen siya da siyarwa.
Idan kunne yaji jiki ya tsira, Allah ya sa mu gyara halayenmu mu da kanmu kafin mu zargi shugabanninmu ameen.
Sakon
Editan Alfijir labarai
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj