Ajali! Wani wawan naushi yayi sanadiyar mutuwar wani mai rabon fada a Adamawa

Dambe

Wani mai suna Markus Dali mazaunin Sina Kwande a karamar hukumar Michika a jihar Adamawa ya rasa ransa yayin da ya ke kokarin rabon faɗa tsakanin wasu mutane biyu.

Alfijir labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta lokacin da Dali ya shiga tsakanin Barka Yama da Alex Z. Tari domin ya raba su faɗa.

Daily Trust ta tattaro cewa Barka ya kawo naushi sai ya samu Dali wanda hakan ya sa ya fadi sumamme, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti.

An kama wanda ake zargin mai shekaru 32, Barka, kuma an tuhume shi da laifin kisan kai a karkashin sashe na 191 na kundin laifuffuka.

A wata kotun majistare da ke Yola, dan sanda mai shigar da kara, ASP Francis Audu, ya ba da labarin yadda lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa Dali ya yi kokarin raba masu fadan biyu amma Barka ya yi masa mugun rauni.

Alkalin Kotun,  Majistare Muhammed Njidda ya bayar da umarnin tsare Barka a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da ake jiran shawarar shari’a daga ma’aikatar karɓar kararrakin jama’a.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *