Rikici Ya Balle A Masallaci Marigayi Dr Ahmad Bamba Kano

Alfijr ta rawaito wani rikicin jagoranci ya tilasta rashin yin sallar Jumu’a a Masallacin Darul Hadith na marigayi Dr. Ahmad Ibrahim BUK.

Tarzoma ta kaure a Masallacin ne lokacin da sabon liman zai hau Mumbari don soma huɗu ba, inda wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna ƙin amincewa da shi, lamarin da ya kawo rikici.

Tuni aka rufe masallacin tare da baza jami’an tsaro a kofa da kewayensa.

Yanzu haka dai tuni ɓangarorin biyu suka nufi shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin sasantawa.

Freedom Radio

9 Replies to “Rikici Ya Balle A Masallaci Marigayi Dr Ahmad Bamba Kano

  1. Subhanallah!!
    Abu bai yi ba, ace saboda son shugabanci a kasa yin Sallar Juma’a. Ya kamata mu rika sanya hakuri a rayuwa.
    Wallahi ban ji dadi ba.

  2. Subhanalla, abunnan dai mana dadiba kamata ayiwa Wanda ya assasa masallacin adalci akauda bambamci da domin Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *