Kotu Ta Tabbatar Da Dauda Lawal A Halastatcen Ɗan Takarar PDP A Zamfara

Daga
Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta yi zamanta na yanke hukunci Kan shari’u da ke gabanta na Dauda Lawal Dare da Ibrahim shehu Bakauye .

A hukuncin Kotun na yau ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2023 a jihar Zamfara.

Don haka, kotun ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Gusau ta yanke wanda tun farko ta soke Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP.

Idan dai za a iya tunawa, Engr Ibrahim Shehu daya daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamna ya maka Dauda Lawal kotu bisa abin da ya kira rashin bin ka’ida a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *