Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani game da wannan iƙirari na shugaban NNPP yayi, yana mai cewa Shugaban Ƙasa Tinubu na da alaƙa mai kyau da duka ɓangarorin biyu “musamman ma Muhammadu Sanusi II”.
Alfijir labarai ta ruwaito daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Abdu’aziz Abdul’aziz ne ya ƙara da cewa maganar zargi ne kawai “maras tushe”.
“Abin da mai maganar bai sani ba ko kuma bai faɗa ba saboda siyasa shi ne; shugaban ƙasa na da alaƙa mai kyau da duka waɗanda ke taƙaddama a kan wannan sarauta,” in ji shi.
“Musamman ma Sarki Sanusi II, wanda suke da alaƙa tun lokacin da ya nemi sarautar a 2014. Kuma ya sani cewa Sarki Aminu Ado bai taɓa zuwa ya ga Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa ba tun lokacin da ya hau mulki.
Shugaban NNPP na Kano ya bayyana hujjar cewa Tinubu na da hannu a rikicin masarautar kano
“Amma Sanusi II ya zo ba sau ɗaya ba kuma ya ga shugaban ƙasa. Wannan ya nuna irin alaƙar da ke tsakaninsu. Wani mutum ya fito yana magana a kan wani abu da ba shi da hujja abin takaici ne.”
Ko a baya-bayan nan ma sai da musayar kalamai ta ɓarke tsakanin fadar Bola Tinubu da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa kwankwaso, kan zargin da Kwankwason ya yi cewar gwamnatin Tinubun na ƙoƙarin ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar Kano.
Yayin wani taron ƙaddamar da aiki da gwamnatin jihar Kano ta gudanar, an jiyo Kwankwaso na zargin cewa “wasu sun haɗa baki da jagororin jam’iyyar APC suna ƙoƙarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da fitina, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci”.
Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin zargi marar tushe ballantana makama.
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
Allah ya kyauta