Rufe matatun man Najeriya mataki ne da zai kawo karshen yaudarar kai – In Ji Ojulari

FB IMG 1770824758594

Shugaban rukunin kamfanin man fetur na ƙasa NNPC, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa rufe matatun man fetur mallakin gwamnati wani muhimmin mataki ne na kawo ƙarshen abin da ya kira “shekaru na yaudarar kai” a ɓangaren tace mai ga ƙasa.

Ya faɗi haka ne yayin taron Nigeria International Energy Summit (NIES), inda ya ce Najeriya ta shafe lokaci mai tsawo tana nuna kamar matatunta na aiki yadda ya kamata, alhali a zahiri ba sa samar da gagarumar fa’ida.

Najeriya na da matatun mai huɗu mallakinta, waɗanda suka gaza aiki yadda ya kamata.

Sai dai duk da haka, gwamnatoci daban-daban sun ci gaba da ware kuɗaɗe domin gyaransu ba tare da an ga sakamako mai kyau ba.

Ojulari ya ce binciken da NNPC ya gudanar ya nuna cewa aikin matatun ya koma tamkar al’ada ce kawai, ba kasuwanci ba.

“Muna tafiyar da tsari ne kawai, ba kamfani ba,” in ji shi. “Kuɗi na fita, amma babu ƙimar da ke dawowa.”

Ya ƙara da cewa ba a ɗauki matakin rufewar cikin sauƙi ba, la’akari da muhimmancin da matatun ke da shi a zukatan yan Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *