Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta rufe wasu hanyoyin ne da suke dangana mutane da gidan sarki na Nasarawa dake kan titin zuwa gidan gwamnati saboda bayanan sirri da suka samu na kokarin kawo hargitsi a jihar.
“Mun sami bayanan sirri dake tabbatar da cewa wasu mutane na son yin zanga-zangar da za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali, hakan ta sa rundunar ‘yan sandan tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro suka baza jami’ansu zuwa wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano domin hana zanga-zangar da kuma tabbatar da tsaron jama’a”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya turawa manema labarai.
Ya ce “A sakamakon wadannan matakan da aka dauka, an kama wasu mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka, kuma ana ci gaba da bincike.
Rundunar zata tabbatar ta gurfanar da wadanda ake zargi da aikata wannan tashin hankali a gaban kuliya.
Rundunar ta gargadin daidaikun mutane da kungiyoyi game da yin duk wani nau’i na taro, jerin gwano, bisa ka’ida ba. Kaucewa Wannan gargadi zai iya sawa jami’an tsaro su dauki mataki.
Kiyawa ya yi kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga jami’an tsaro na duk wani abu da ba su aminta da shi ba, haka kuma Rundunar ta yaba da hadin kai da goyon bayan mutanen jihar Kano ke ba ta a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya.
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ