Daga Aminu Bala Madobi
Babban Malamin Addinin Musulunci Sheikh Karibulla Sheikh Nasir Kabara ya yi Kira ga Wakilan alumma da su kasance masu bin tafarki da tanadin addini don kaucewa fushin Allah da kuma alummar da suke wakilta.
Alfijir labarai ta ruwaito Malam Kharibu Nasir Kabara ya bayyana haka ne yayin taron gangamin masu mu amala da kafar sadarwa Qadiriya Media Connect 2024 da aka Gabatar a Jihar Kano.
Nasir ya ce matukar suka dora hannu akan wannan doka da aka lullubo aka kawo to zasu ga fushin alummar da suke wakilta lokacin da suke da bukata.
Babban malamin ya jaddada cewa an dade ana yin abubuwan da basu dace ba a kasar nan ana yin shiru.
“To muna amfani da wannan dama mu gayawa masu ruwa da tsaki cewa bazamu sake lamuntar irin wannan aika aikar ba”
“A m gayawa duk masu ruwa da tsaki cewa BAMU YARDA BA, KUMA BAZAMU YARDA BA. idan kasan kai wakili ne na alumma to kayi damarar kare alummar ka tun yanzu” Nasir in ji shi.
Ya roki masu amfani da kafar sadarwa da su fi maida hankali akan abunda zai Samar musu da lada bayan mutuwar su.
Ya kara da cewa ba kowanne lamari ne dan musulmi zai dauka a matsayin abun cigaba ba, kamata yayi mutum ya duba wanda zai amfaneka Duniya da lahira.
Daga karshe sheshin malamin ya ja hankalin mahalatta taron dasu yi amfani da kafar sadarwa wajen kawo wa kasa zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki da kare addinin musulunci.
Yayin gangamin, Nasir kabara ya bukaci alummar musulmi dasu cigaba da adduoi domin samun saukin rayuwa da fita daga halin matsin da talakawa suke ciki.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj