Babbar Magana: An Karanto Kudirin Kirkiro Sabuwar  Jihar Etiti Karo Na Farko A Majalisar Najeriya

IMG 20240708 WA0075

Daga Aminu Bala Madobi

An gabatar da kudirin dokar kafa jihar Etiti a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar nan a zaman da aka yi ranar Talata.

Alfijir labarai ta ruwaito yan majalisar wakilai guda biyar ne suka dauki nauyin wannan sabon kudiri da suka hadar da — Hon. Amobi Ogah Miriam Onuoha, Kama Nkemkama, Chinwe Nnabuife, da Anayo Onwuegbu.

Kudirin na da nufin za a kirkiro sabuwar jihar ne daga sassan jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, da Imo.

A cewar binciken sabuwar jihar Etiti za ta ƙunshi kananan hukumomi 11 daga waɗannan jihohi biyar, tare da babban birnin ta dake Lokpanta.

Kudirin ya bukaci a gyara wasu sassa uku na kundin tsarin mulkin 1999 don maye gurbin jihohi “36” da “37” a cikin jerin jihohin da kuma kara “Etiti” a jadawalin jerin jihohin Najeriya bayan “Enugu.”

Menene ra’ayinku kan wannan sabuwar jiha da ake kokarin kirkiro wa daga shiyyar nyamurai?

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *