Jigo a jam’iyyar APC a Kano, Sanata mas’ud El-jubril Doguwa ya fice daga jam’iyyar a jiya alhamis.
Sanata Doguwa ya bayyana ficewar ta sa ne daga APC a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.
“Ina sanar da ku cewa mun dauki wannan matakin ne da yawun dukkanin masoya da magoya bayan mu, saboda munanan manufofin jam’iyyar APC na kuntatawa talakawa.
Sanata Doguwa ya ce sun shiga APC ne a tunaninsu tun da suna da goge kan harkokin siyasa, za a rika tuntubarsu don ba da shawarwarin da zasu ciyar da jam’iyyar da kasa gaba.
Idan har Siyasa zata zama haka ace yan siyasa da suke da kwarewa ba za a rika basu wani aiki da zasu yi amfani da gogewarsu ba wajen kawo cigaba, to sai muce kaicho.
SERAP ta bai wa gwamnoni wa’adi su mayar wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu
An Yanke Wa Mutane 106 Hukunci Cikin 149 Da Yan Sanda Suka Gurfanar A Kano
Ya ce jam’iyyar APC ta basu kungiya saboda manufofin da gwamnatin APC take aiwatarwa wadanda suka sanya talakawa cikin mawuyacin hali.
Sai dai Sanata Doguwa bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba, bayan sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC.
Sanata mas’ud El-jubril Doguwa dai dan karamar hukumar doguwa ne dake yankin Kano ta kudu a jihar kano Nigeria.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj