Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana ibtila’in ambaliyar ruwan da aka samu a Maidugurin jihar Borno da cewa wani babban abu ne da ya girgiza al’umar Kasar nan baki daya.
Alfijir Labarai ta rawaito Alh Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a sakonsa na jajantawa al’umar jihar Borno da Kasa baki daya bisa ambaliyar ruwan data faru a jihar.
Yace ba kasafai aka fiya samun irin wannan mummunan ambaliyar ba, amma idan hakan ya faru to babu abunda ya kamata ga al’uma sai yin addu’ar Allah Kada ya sake maimatawa.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma bada lafiya ga wadanda suka jikkata tareda mayar da mafificin alheri ga wadanda suka rasa dukiyoyinsu.
Daganan mai Martaba Sarkin ya sake Mika jajensa ga Shugaban Kasa chief Ahmad Bola Tinubu da Mataimakinsa Alhaji Kashim Shetima da Gwamnan jihar Borno Professor Baba Gana Umara Zulum da Shehun Borno Alhaji Mustapha El Garbai.
Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa chief Press Secretary to His Highness the Emir of Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj