Sharia! Lauyoyi 500 sun yi alƙawarin kare Gawuna a Kotun Ƙoli

FB IMG 1695548443044


Kimanin lauyoyi masu zaman kansu 500 ne suka yi alƙawarin kare, Nasir Yusuf Gawuna a kotun koli.

Alfijir labarai ta rawaito Joseph Onwudiwe, mai magana da yawun lauyoyin a karkashin kungiyar masu kula da dimokuradiyya da doka ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a yau Talata.

Mista Onwudiwe ya ce an yi hakan ne domin inganta dimokuradiyyar kasar.

“Yan Najeriya sun lura sosai da halin da ake ciki a jihar Kano dangane da zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris.

“A matsayinmu na kungiyar da ke da alhakin kare mutuncinmu da dabi’unmu na dimokuradiyya, yanzu ba mu gamsu da hare-haren maganganu marasa dadi da ake kaiwa bangaren shari’a ba.

“Kuma wani yunƙuri na bata wa Kotun suna ba. Ba za mu sake naɗe hannayenmu a matsayin lauyoyi ba, mu kalli yadda ake ci gaba da cin zarafi da cin mutuncin sashen shari’a ba,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

One Reply to “Sharia! Lauyoyi 500 sun yi alƙawarin kare Gawuna a Kotun Ƙoli”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *