Shekaru 75 Na Ganduje, Na Cigaba Da kawo Sauyi A Rayuwar Al’umma  – in  Ji Dr Bello

Bello

Tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSSMB), Dakta Bello Shehu, ya taya murna ga Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa cika Shekaru 75 masu albarka.

A cikin wata sanarwa da Shehu ya sanyawa hannu ya bayyana Ganduje a matsayin “babban dan kishin kasa, shugaba mai hangen nesa, kuma jagora mai tausayi.”

“Ranka ya dade, shugabancinka a matsayinka na tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma a yanzu a matsayinka na Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, ya bar babban tarihi a fagen siyasar Najeriya,” in ji Dokta.

Shehu ya bayyana irin gudunmawar da Dr. Ganduje ya bayar a fannin ilimi, kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, inda ya bayyana cewa, “Jajircewar ka abin a yaba ce wajan ci gaban jihar Kano, musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, na ci gaba da zaburar da al’umma baki daya.

Tunda farko da yake tsokaci kan zamansa a gwamnatin Dakta Ganduje, Dokta Shehu ya bayyana goyon bayansa ga ayyukan ilimi da Gwamna ya bayar, inda ya ce, “A matsayina wanda nasami kaina nayin aiki a gwamnatin ka, na sadaukarwar da ka yi wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano da kuma goyon bayan ku ga shirye-shiryen da suka daukaka bangaren ilimi.”

Dokta Shehu ya yi godiya tare da addu’ar Allah ya kara wa Dakta Ganduje nasara da lafiya, inda ya ce, “Hikimar ku, da jajircewa, da iya hada kan jama’a su ne abin da ya karfafa gwiwar mu baki daya.

Ina fata tareda rokon Allah (SWT) ya kara maka lafiya da hikima da karfin gwiwa.”

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *