Shugaba Buhari Ya Buɗe Soron Ingila A Masarautar Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero,ya yabawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa ziyarar buɗe Soron Ingila da kuma aminta da yayi wajen Karin kwanaki 10 da cikar wa’adin daina karbar tsoffi takardun kudi da babban bakin Kasa CBN ya shirya yi.

Soron Ingila Masarautar Kano

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarce shi a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero, yace Karin wa’adin kwanaki 10 da akayi ya nuna alamar cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jin koken al’ummar Kasar nan duba da yanda al’umma suke shan wahala a wajen janji kudi.

Ya Kuma Kara da cewa,yayin yakin neman zabe ayi amfani da hanyoyin da za a ji koken al’umma.

Sarkin yayi addu’ar Allah yasa ayi zabe lafiya a gama lafiya ba tare da ansamu wata fitina ba.

Da yake jawabi,shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace ya ziyarce Masarautar Kano ne domin kawo gaisuwa ga mai martaba sarki da kuma bude wasu aiyuka da gwamnan kano yayi.

Tunda farko sai da shugaban kasa Muhammadu Buhari sai da ya Bude ya bude fadar Soron Ingila da aka sake Sabunta gininta.

Soron Ingila, fada ce mai tsohon tarihi da Marigayi Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya ginata a shekara ta 1934, yayin da a shekarar 2022 Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya sabunta ginin fadar tareda fadada ta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *