Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Hukuncin Da Kotun Kolin Tayi aKan Kananan Hukumomi.

FB IMG 1719960146800

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaba Bola Tinubu ya yabawa hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke na tabbatar da manufar kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na baiwa kananan hukumomi damar tasarrafi da kudadensu.

Alfijir labarai ta ruwaito cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya bayyana cewa babban kalubalen ci gaban al’ummar kasar nan tsawon shekaru shi ne rashin gudanar da ayyuka a kananan hukumomi yadda ya kamata.

“Manufar shirin mu shine ya shafi al’ummar kasar nan, a kowane mataki, ba tare da la’akari da addini, kabila, jinsi ko, bangarancin siyasa ba.

“Gwamnatina ta kai wannan karar ne domin tayi imanin cewa dole ne mutanenmu su samu sauki, kuma hukuncin da aka yanke a yau ya tabbatar da cewa jami’an kananan hukumomin da jama’a suka zaba ne kawai za su mallaki dukiyar al’umma, wannan hukunci ya tabbata a fili cewa za mu iya amfani da hanyoyin da suka dace wajen gyara kasar mu da sake fasalin tattalin arzikinmu don ganin Nijeriya ta zama wani dandali mai kyau da kuma adalci ga daukacin al’ummarmu,” in ji Shugaban.

Tinubu ya kara da cewa samar da wasu muhimman ababen more rayuwa da kayayyakin jama’a, kamar ginawa da kula da wasu hanyoyi, tituna, fitulun tituna, magudanun ruwa, wuraren shakatawa, lambuna, wuraren bude ido, da sauran su.

Don haka ya tabbatar da cewa hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da ‘yancin da kundin tsarin mulkin kananan hukumomi ya ba shi, dangane da ‘yancin cin gashin kai na harkokin kudi, da sauran muhimman ka’idoji, yana da matukar muhimmanci a tarihi kuma yana kara karfafa kokarin da ake yi na inganta tsarin tarayyar Najeriya na gaskiya don ci gaban kasa baki daya.

Tinubu ya kuma yabawa Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Mista Lateef Fagbemi (SAN) bisa jajircewarsa da kishin kasa kan wannan muhimmin aiki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

Khttps://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *