Shugaba Tinubu Ya Nada Farfesa Attahiru Jega  Sabon Mukami

FB IMG 1720590524216

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan aiwatar da sauye-sauye a harkar  kiwo don magance matsalolin da ke kawo cikas ga noma da kuma  samar da karin damarmaki da za su amfani  manoma, da makiyaya, da duk wadanda ke da hannu a harkar noma da kiwo.

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban ya nada tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.

Tinubu ya jaddada cewa aiwatar da sauye-sauyen zai bukaci hadin kan mambobin kwamitin, wadanda suka fito daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu, da gwamnonin jihohi, da dukkan ‘yan Najeriya.

“Zan yi kira ga dukkanmu da mu cire siyasa ko bangaranci a wannan harkar. Zan zama shugaban kwamitin sannan Farfesa Jega ya kasance a matsayin mataimakina“.

“Wannan ba batun siyasa ba ne; dama ce ta cigaban kasa, duk da yake ba zan kasance a wajen gudanar da ayyukan kwamitin  a koda yaushe ba, Farfesa Attahiru Jega zai cigaba da jagorantar kwamitin domin inganta manufofinmu,” in ji shugaban.

Da yake kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa, Tinubu ya godewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na hada kwararru da za su samar da damammaki a fannin kiwo. , inda ya bayyana cewa, za a samar da ma’aikatar kula da kiwon dabbobi domin kara yin nazari a kan abubuwan da ake da su a yankin.

Shugaban ya yi nuni da cewa, akwai bukatar kawo sauye-sauye a tsarin kiwon dabbobi na gargajiya tare da goyon bayan masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnatocin Jihohi, domin samar da sabbin hanyoyin bunkasa harkar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *