Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohon Sanatan Kano Ta tsakiya Mukami

FB IMG 1720814344337

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Sanata Bashir Garba Lado a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa .

Alfijir labarai ta ruwaito mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Asabar.

Shugaban ya bayyana Lado Mohammed a matsayin gogaggen dan siyasa kuma dan kasuwa daga jihar Kano.

Muhammad Bashir Garba Lado tsohon Sanata ne da ya wakilci Kano ta tsakiya, kuma tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa.

Ajuri ya ce Shugaba Tinubu β€œyana tsammanin sabon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa zai yi amfani da kwarewarsa wajen inganta alakar dake tsakanin bangaren zartarwa da majalisa dattawa.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *