‘Yancin Kananan Hukumomi:Kungiyar Gwamnoni Sun Magantu

IMG 20240608 WA0001

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnonin Najeriya sun amince da hukuncin da kotun koli ta yanke a kan yancin cin gashin kananan hukumomi, sun ce huta roro su an saukaka musu ne.

Alfijir labarai ta ruwaito gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya AbdulRazaq AbdulRahman ya bayyana cewa kungiyar ta yi maraba da hukuncin da kotun koli ta yanke na baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu.

Ya yi wannan jawabi ne a fadar gwamnati da ke Abuja tare da rakiyar takwarorinsa na Bauchi da Bala Mohammed dana Imo  Hope Uzodimma.

Idan za ku tuna a ranar Alhamis ne kotun koli ta bayyana cewa bai dace gwamnonin jihohi su rike kudaden da ake warewa kananan hukumomi.

Kwamitin mutane bakwai, a hukuncin da mai shari’a Emmanuel Agim ya yanke, ya bayyana cewa ya kamata kananan hukumomin kasar 774 su sarrafa kudaden su da kansu.

Kotun kolin ta ce ikon gwamnati ya kasu kashi uku na gwamnatin tarayya, jiha da kuma kananan hukumomi.

“Muna maraba da hukuncin da kotun koli ta yanke. An ba da yarda kuma manyan lauyoyin mu sun nemi oda wanda za mu yi nazari cikin nutsuwa. Amma gaba daya, gwamnonin sun ji dadin yadda aka maida madafun iko dangane da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi,” in ji shugaban

Gwamna Abdul Razak ya ce kungiyar gwamnonin Najeriya za ta yi taro a ranar Laraba mai zuwa domin fitar da matsaya kan lamarin. Ya ce sabanin rade-radin da akeyi, gwamnonin ba su taba yin cushe akan kudaden kananan hukumomi ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *