Shugaban Amurka Joe Biden Ya Yiwa Duk ‘ƴan Wiwin Ƙasar Afuwa


Alfijr ta rawaito shugaba Joe Biden ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis cewar ya yi afuwa ga duk Amurkawan da kotunan tarayya samu da laifin kama su da tabar wiwi”.

Alfijr Labarai

Biden ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi da su yi hakan.

Akwai dubban mutanen da a baya aka yanke musu hukuncin za a iya hana su aikin yi, ko mallakar gidaje, ko kuma damar karatu a sakamakon laifin tabar wiwi a baya afuwana zai kawar da wannan nauyi. In Ji shi

“Na biyu: Ina kira ga gwamnoni da su yafe laifukan mallakar tabar wiwi na jihar.

Kamar yadda babu wanda ya isa ya kasance a gidan yarin tarayya don kawai ya mallaki tabar wiwi, babu wanda ya isa ya kasance a gidan yari na gida ko gidan yarin jaha saboda wannan dalili.

Wannan shine kafin ku magance bambance-bambancen kabilanci game da tuhuma da yanke hukunci.

Alfijr Labarai

Biden ya kara da cewa, a yau, mun fara gyara waɗannan kuskuren.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *