Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewar, ƙasarsa na iya ɗaukar matakin soja a Najeriya idan gwamnatin ƙasar ta ci gaba da barin ana kisan Kiristoci.”
Trump ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Asabar.
Wannan na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar damuwa kan ‘yancin addini (Country of Particular Concern) saboda abin da ya kira “kisan gilla ga Kiristoci.”
A cikin sabon jawabin nasa, Trump ya kuma bayyana cewa Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi da taimako da take bai wa Najeriya, matuƙar gwamnatin ƙasar ta gaza ɗaukar mataki kan abin da ya kira “ta’addanci da zalunci ga Kiristoci.”
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t