Daga Aminu Bala Madobi
Tigran Gambaryan, shugaban rukunin kamfanin kudi na crypto Binance, wanda aka tsare a Najeriya na tsawon watanni, ya bayyana sunayen wasu ‘yan majalisar dokokin Najeriya uku da ake zargi da neman cin hancin dala miliyan 150 (kimanin N225bn a ranar 14 ga Fabrairu).
Idan za a iya tunawa a watan Janairun 2024, gwamnatin Najeriya ta tsare Gambaryan da wani jami’in Binance, wadanda suka zargi kamfaninsu da karkatar da kudade da kuma karfafa aikata laifuka a Najeriya.
Sai dai an sake shi bayan gwamnati ta yi watsi da tuhumar da ake yi masa biyo bayan shigar da gwamnatin Amurka ta yi.
Shugaban na Binance, a lokacin da ake tsare da shi, ya ambaci cewa wasu ‘yan majalisar sun bukaci a ba su cin hanci don hana kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.
Shugaban kamfanin A ranar Juma’a, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X. Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin dasuka hadar da Peter Akpanke, Philip Agbese da Ginger Obinna Onwusibe.
Wani abin ban mamaki, Onwusibe ne ke jagorantar kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa karkashin kakakin majalisar.
Ana ci gaba da kokarin ganin wadanda ake tuhumar su yi jawabi amma a baya majalisar ta ki amincewa da neman cin hanci daga shugaban na Binance.
A cikin sakon nasa, Gambaryan ya bayar da cikakkun bayanai kan bukatar cin hancin, ciki har da ranar da abin ya faru da kuma yanayin da aka nema.
“Hukumar DSS ta shiga cikin lamarin majalisar wakilai Mun gana da su a ofishinsu a ranar Juma’a 5 ga watan Janairu, 2024, a matsayin sharadi na ganawar mu da ‘yan majalisar wakilai. Sun yi ishara da cewa dole ne mu bi duk abin da ‘yan majalisar suka umurce mu da mu yi.
“A taron majalisar wakilai uku ne suka halarta. Biyu daga cikinsu su ne Peter Akpanke da Philip Agbese, wadanda ke aiki karkashin Ginger Obinna Onwusibe. Akwai dan majalisa na uku, amma ban tuna sunansa ba”. Inji sa
” Sun kafa kyamarori da kafofin watsa labarai na karya don sa taron yayi armashi mu saki jiki don basu cin hanci ba a hukumance ba, amma kyamarorin ba su ma kunna su ba.
“Sun nemi cin hancin dalar Amurka miliyan 150, wanda aka biya cikin asusun ajiyar cryptocurrency cikin wallet ɗinsu na sirri.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ