Shugaban Jami’ar FUDMA Ya Zargi Wasu Ma’aikatansa da Taimakawa Ƴan Bindiga

FB IMG 1720591924108

Shugaban Jami’ar Dutsinma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Bichi, ya zargi wasu ma’aikatan jami’ar da taimakawa ƴan bindiga da bayanai. Yankin na fama da hare-haren ƴan bindiga inda ake garkuwa da ɗalibai, da ma’aikata, da kuma iyalansu.

Alfijir labarai ta ruwaito a wani hari na baya-bayan nan, an kashe Dr. Tiri Gyan David, shugaban sashen Tattalin Arzikin Noma, Yada Albarkatun Ƙasa, da Raya Karkara, sannan kuma an yi garkuwa da ƴaƴansa.

Farfesa Bichi ya bayyana cewa shugabancin jami’ar ya gano ma’aikatan da ake zargi da taimakawa ƴan bindiga da bayanai, kuma sun miƙa lambar wayarsu ga hukumar tsaro domin bincike.

Duk da haka, Farfesan ya nuna damuwarsa kan rashin bayyana cikkaken rahoto daga hukumar tsaro. Ya jaddada cewa jami’ar na ƙoƙarin hana sake faruwar irin wannan al’amari, amma lamarin na ƙara ta’azzara.

Leadership Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *