Shugaban Najeriya ya aiko mataimakinsa jihar Kano domin jajantawa ƴan kasuwar Singa

IMG 205315 15226 1771185293139

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kano bisa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin jajantawa da kuma tallafa wa waɗanda gobarar kasuwar Singa ta shafa.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, da ya sanar da haka a ranar Lahadi, ya ce tawagar, wadda za ta taso daga Abuja gobe, za ta miƙa saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga yan kasuwar da suka yi asarar biliyoyin Naira sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar.

A madadin gwamnatin tarayya, tawagar za ta kuma yi alƙawarin bayar da tallafin kuɗi domin taimaka wa ƴan kasuwar da abin ya shafa, tare da tallafa wa gwamnatin jihar Kano wajen gaggauta buɗe kasuwar domin komawa harkokin kasuwanci.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *