Shugaban Najeriya ya sake magantuwa a kan ƙudurin gyaran haraji da ya kai majasa

FB IMG 1729698661292

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ba zai janye ƙudurin dokar gyaran haraji daga gaban majalisar dokokin ƙasar ba, duk kuwa irin irin ce-ce-ku-cen da ƙudirin ya janyo a ƙasar.

Alfijir labarai ta rawaito Ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ne ta fara bayyana damuwa tare da watsi da ƙudirin saboda a cewarsu ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohin arewacin ƙasar,

Haka ma ita ma majalisar tattalin arzikin ƙasar a zamanta na ranar Alhamis ta yi kira ga shugaban ya janye ƙudirin.

Majalisar tattalin arzikin, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, tare da gwamnonin jihohin ƙasar 36 a matsayin mambobi ta bayar da shawarar janye ƙudirin, domin bayar da isasshen lokaci na tattaunawa da tuntuɓar juna a tsakanin masu ruwa da tsaki kan harajin.

To sai dai cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce shugaban ya ji duka koken da ake yi game da ƙudurin da buƙatar janye shi da ake yi, to sai dai ya ce ƙudirin – wanda tuni aka fara muhawara a kansa a majalisar – ba za a janye shi ba, sai dai ya ce a iya yin wasu gyare-gyare a lokacin muhawarar majalisar da kuma jin ra’ayin jama’a.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar bai aike da ƙudurin gaban majalisar ba, har sai da ya kafa kwamitin wanda kuma ya yi aiki na tsawon shekara guda yana tattara ra’ayoyi game da ƙudirin daga wajen masu ruwa da tsaki a fannin fannin arziki daga duka ɓangarorin ƙasar.

”Shi wannan ƙudiri da ke gaban majalisa, an aika shi domin kawo gyara a fannin yadda ake tafiyar da karɓar haraji a ƙasarmu”.

Domin samun sauran shirye shiryenmu👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *