Shugabar Jam’iyyar Conservative A Ingila Ta Caccaki ‘Yan Sandan Nijeriya

Kemi

Daga Aminu Bala Madobi

Shugabar Jam’iyyar Conservative ta Burtaniya Kemi Badenoch ta zargi ‘yan sandan Najeriya da yin fashi da makami kan wadanda ya kamata ace sun kare.

Alfijir labarai ta rawaito Shugabar ta zargi ‘yan sandan Najeriya da yi wa ‘yan kasa fashi maimakon kare su. A cewar jaridar The Niche, Badenoch ta yi wannan tsokaci ne yayin wata ganawa da ‘yan jaridu a Birtaniya.

‘Yar jaridar Birtaniya ta tambaye ta ko ta amince da ‘yan sandan Birtaniya. A martanin ta, ta ce: “Na yi amanna da su. Amma ‘yan Sandan Nijeriya tabb.

“Zuwa na Burtaniya, naga gogewa da ‘yan sandan Burtaniya na da kyau kwarai. “Tabb amma ‘Yan sanda a Najeriya za su yi maka fashi ne da sunan kare ka (‘Yan jaridun suka kama shewa da dariya).

“Na tuna lokacin da ‘yan sanda suka sace takalmin ɗan’uwana da agogonsa.” inji Badenoch  ‘Yan Jaridun Birtaniyya suka razana don mamaki cikin kaduwa. “Sun dauki takalminsa da agogon hannunsa?”

Kemi ta ci gaba da cewa: “Kasar matalauta ce. Mutane suna yin abinda suka ga dama abubuwa iri-iri. Don haka, ana baiwa mutane bindiga lasisi ne kawai don tsoratarwa. Amma wannan ba shine kawai matsalar ba. Wannan ba shine abinda ya kamata mu yi amfani da shi ga ‘yan sandan Burtaniya ba.

“Lokacin da aka yi min fashi, alal misali, ’yan sanda suna wurin. Sun taimaka kafin daga bisani su kama mutumin. Wannan ya faru a cikin 2004, wato shekaru 20 da suka gabata.

Idan za a iya tunawa, jawaban Badenoch ya tayar da hazo a dandalin sada zumunta game da alakar ta da Najeriya biyo bayan sukar da ta yi kan harkokin mulkin kasar da kuma al’umma.

A wata hira da ta yi, ta bayyana Najeriya a matsayin “kasa mai ra’ayin gurguzu da ke cike da barayin ‘yan siyasa da rashin tsaro”.

Sukar da Badenoch ta yi wa Najeriya ya dauki hankalin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya yi tir da irin yadda ta ke fassara Najeriya.

Shettima ya kuma shawarci Badenoch da ta canza sunanta idan har tana son sanin kasarta. Sai dai mai magana da yawun Badenoch a martani ga Shettima ya ce ‘yar siyasar a tsaye take kan kalaman ta kuma ita ba PR ba ce ga Najeriya.

“Kemi ba ta da sha’awar yin aikin sadarwa PR na Najeriya; ayanzu ita ce shugabar ‘yan adawa a Burtaniya,” in ji kakakin.

“Ta fadi gaskiya. Ba za ta janye kalaman ta ba, kuma ta tsaya kyam kan abin da ta ce. ” Kwanan nan, Badenoch ta ce ta fi sanin kabilar Yarbawa fiye da na Najeriya.

‘Yar majalisar dokokin Burtaniyar ta ce tana alfahari da kakaninta na Yarbawa wanda ya ba ta “karfi sosai”.

Shugabar masu ra’ayin rikau ta ce “ba ta da wani abu da ya hada ta” da ‘yan Najeriya daga yankin arewacin kasar.

“Bani da wani abu da ya hada ni da mutanen arewacin kasar nan, ‘yan Boko Haram suke , amma duk da haka an dunkule ku da guri guda.”

An haifi Badenoch a Birtaniya a shekarar 1980, iyayen ta Yarabawa ne daga Najeriya. Ta koma Najeriya, inda ta girma. A ƙarshe Badenoch ta tafi Burtaniya lokacin da ta cika shekaru 16.

‘Yar siyasar mai shekaru 44 ta yi aiki a matsayin sakatariyar harkokin kasuwanci kafin zaben ta a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative. Ta kasance mai tsaurin ra’ayi game da shige da fice kuma hakan ya ba ta damar adawa ga masu mulkin mallaka na Burtaniya a baya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *