Daga Rabi’u Usman
Kwamishinar ma’aikatar mata kananan yara da masu bukata ta musamman ta jihar kano Haj Aisha Lawan Saji rano ta bayar da tallafin jari na Naira Dubu 30 ga kowacce mace, domin gudanar da sana’oin dogaro da kai da inganta rayuwar su, ga mata masu larurar yoyon fitsari 200 a jihar kano a wani bangare na cigaba da ranar yaki da cin zarafin mata da kananan yara ta duniya.
Taron ya gudana ne a harabar inda aka ajiye masu yoyon fitsari a kwaryar birnin kano, inda Gidauniyar Fistula ta koyar da mata 200 sana’oin dogaro da kai domin samun damar taimakawa ‘yayan su da inganta rayuwar su musamman wadanda suke kula da su.
Kwamishinar tayi kira ga mata dasu dinga zuwa yin awo asibiti domin tabbatar da lafiyar su kafin Haihuwa domin gudun kamuwa da larurar yoyon fitsari.
Aisha Saji tana daga cikin kwamishinonin da suka samu sauyin ma’aikatu a jihar kano, Wanda gwamnatin kano ta mayar da ita ma’aikatar kula da yawon Bude idanu da raya Al’adu ta jihar kano.
Wakilin mu ya zanta da Aisha Lawan Saji inda ta bayyana yanda shirin ya gudana tare da yin kira ga wadanda suka rabauta da tallafin domin yin amfani da shi ta hanyar da ta dace harma da karfafa musu gwiwa wajen zuwa asibiti domin tabbatar da koshin lafiyar su.
Shugabar dake kula da gidan masu yoyon fitsari ta jihar kano Aisha Sani kurawa ta mika Godiya ga gwamnatin kano musamman ma’aikatar mata kananan yara da masu bukata ta musamman a madadin mutanen da suka rabauta da tallafin kudin da za su ja jari domin dogaro da kawunan su, tana mai cewar wannan shi ne karo na farko da aka ta6a baiwa masu larurar yoyon fitsari tallafi a jihar kano.
Ta kara cewar, a wannan karon ne suka taba ganin gwamnatin kano ta kula da wadannan mutane.
A nasu bangaren wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun nuna jin dadin su tare da alwashin yin amfani da tallafin kudin wajen yin sana’oin da suka koya.
Inda suka yabawa rano bisa kokarin ta na ganin ta tuna da su a matsayin su na marasa lafiya.
Daga cikin mahalarta taron sun hadar da Daraktar kula da walwalar jama’a ta ma’aikatar mata Haj Binta yakasai da Mataimakiyar shugabar jam’iyyar NNPP ta jihar kano Haj Hauwa Fulani da dai sauran su.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj