Sufeton ‘Yan sanda ya umurci janye jam’in da aka jibge a cikin Kananan Hukumomin Ribas

IMG 20241007 WA0012

Daga Aminu Bala Madobi

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya umurci  a janye jami’an yan sanda cikin gaggawa da aka tura don rufe Kananan Hukumomi 23 na Jihar Rivers.

Alfijir labarai ta rawaito cikin wata sanarwa a ranar Litinin da Grace Iringe-Koko, Jami’ar Hulda da Jama’a ta rundunar ‘Yan Sandan Jihar Rivers ta fitar.

A cewar sanarwar, umarnin ya biyo bayan wasu sabbin abubuwan siyasa da suka faru a Jihar Rivers.

Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Bala Mustapha, ya isar da umarnin IGP Kayode Egbetokun, na janyewar dukkan ma’aikatan ‘yan sanda da aka tura don rufe jihar da kare Ofisoshin Kananan Hukumomi a jihar.”

Sanarwar ta jaddada cewa wannan hukuncin ya dace da kudirin Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya na tabbatar da adalci da kuma cigaba da aikin dimokuradiyya.

Haka zalika ta bayyana cewa za a sake tura ma’aikatan ne kawai idan wani rikici ko rashin tsaro ya faru, inda za a aiwatar da matakan gaggawa cikin sauri don dawo da doka da oda.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Rivers ya tabbatar wa al’umma cewa suna cigaba da dagewa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa za su gudanar da aikinsu cikin kwarewa.

An umarci mazauna da masu ruwa da tsaki dasu cigaba da rayuwar su kamar yadda suka saba cikin natsuwa da bin doka da Oda.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *