Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani babban jami’in hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA tare da hadimin sa a kusa da babban ofishin hukumar da ke kan hanyar Isah-Ogwashi-Uku a karamar hukumar Aniocha ta Kudu a jihar Delta.
Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Juma’a a lokacin da jami’in ke kan hanyar sa ta komawa gida.
Wasu gansu sun bayyana cewa yan bindigan sun yi kwanton bauna ne a kan hanya inda suka tilasta masa shiga wata mota da babu lamba a jikinta.
Da yake magana kan lamarin, wata majiya ta kusa da hukumar ta ce, “Da alama masu garkuwa sun sanya ido ne akan jami’in. wanda hakan ke nuni da cewa sun dade suna bibiyar sa.”
Bincike ya nuna cewa Wannan garkuwa da aka yi shine karo na biyar cikin kwanaki goma da aka yi garkuwa da mutane a garin Ogwashi-Uka.
A cikin wanda ya faru a baya-bayan nan, an harbe wasu matasa biyu har lahira, yayin da wasu biyu kuma aka yi garkuwa da su a hanyar Edo-Otulu da ke Agidiase Quarters. A yanzu haka dai Mazauna garin Ogwashi-Uku sun bayyana fargaba da tsoro game da yadda rashin tsaro ke cigaba da karuwa a yankin.
“Bamu da kwanciyar hankali a yankin mu, Dole ne gwamnati ta yi gaggawar magance wannan matsalar kafin a samu asarar rayuka da yawa,” wani shugaban yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana.
Sai dai kuma Majiyoyin tsaro sun yi nuni da cewa masu garkuwan da alama sun suna da wani makusancin wanda aka sace da ke basu bayani, duba da yadda suka chanza salon garkuwa.
“Da alama dai masu garkuwan suna da wanda ke kawo musu rahoto akan hukumomi” cewar wata majiya.
Da aka tuntubi kakakin hukumar NDLEA reshen jihar Delta, Mista John Kennedy bai ce komai ba game da lamarin. Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka ana ci gaba da kokarin gano jami’in da aka sace tare da hadimin sa .
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj